Ziyarar shugaba Buhari: Kalli dandazon jama'a da suka fito tarban shugaban kasa a Bauchi(Hotuna)

0
36

Shugaban kasa da gwamnan jihar Bauchi yayi da shugaban ya sauka jihar

A jiya alhamis shugaban ya sauka jihar inda zai kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta gabatar

Dandazon jama'a suka fito kwar-da-kwarkwantar su wajen tarban shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da ya kai ziyarar jihar Bauchi.

 

A jiya alhamis shugaban ya sauka jihar inda zai kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta gabatar.

 

Ya samu tarba daga mai karban bako, gwamna Muhammed Abubakar da takwaran shi na jihar Adamawa, Muhammed Jibrila Bindow, tare da sauran jami'an gwamnati, yayin da ya sauka a filin jirgin saman Abubakar Tafawa Balewa.

 

Jim kadan bayan saukar sa, shugaban ya kaddamar da assibitin sojojin sama da aka gina a jihar kana ya ziyarci.

Cikin ayyukan da shugaban zai kaddamar, akwai shirin tallafawa manoman jihar da motocin aikin gona guda 500.

Magoya bayan jam'iyar APC da masoyan shugaban suka fito titunan garin Bauchi domin nuna farin cikin su kan ziyarar da shugaban ya kawo masu.

Kafin zuwan sa, gwamnatin jihar ta kaddamar da ranar alhamis a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar domin su samu damar tarban shugaban.