Super eagles: Tawagar Nijeriya ta shirya damawa da Argentina a wasan sada zumunta da za'a gabatar yau a kasar Rasha

0
127

Tawagar Suoer eagles

Karawan su na sada zumunta tawagar super eagles zata nemi ta kece raini tsakanin ta da Argentina

Tawagar yan kwallon Nijeriya ta super eagles ta shirya karawa da na kasar Argentina a wasan sada zumunta da za'a gabatar a yau talata a birnin Krasnodar na kasar Rasha.

Kwana hudu bayan wasan share fage na shiga gasar kofin duniya ta 2018 da kasar Algeria, yan wasan sun kara zage damtse domin damawa da tawagar Argentina.

 

Za'ayi wasan daidai karfe 5:00 na yamma agogon Nijeriya a filin wasan ta Krasnodar Arena wanda ke iya daukan jama'a 33,000.

Wannan bashi ne karawan su na farko da Argentina a wasannin sada zumunta, wasan su a cikin 2011 a garin Abuja Nijeriya ta samu nasara inda ta doke Argentina 4-1.

Aduwan su na biyu a kasar Bangladesh,  Argentina ta samu nasara inda ta lashe nijeriya 3-1.

Wasan su da Argentina yana cikin shirye-shiryen gasar cin kofin duniya na 2018 wanda za'a gabatar a kasar Rasha. Nijeriya itace kasa ta farko da ta fara samun nasarar shiga sahun kasashe da zasu dama a gasar daga nahiyar afrika.

Nijeriya ta zabi karawa da Argentina bayan kasar Iran da Saudi Arabiya da Morocco sun nemi suyi wasa da ita.