Gasar AMMA: Ali Nuhu da Haliam Atete sune gwarzayen bana

0
49

Jaruma ta amshi kyautar gwarzuwar shekara

Taron gasar na bana wanda shine karo na biyar ya gudana ne a dakin taro dake nan Soli Center a garin Katsina.

Fitattun jarumai Ali Nuhu da Halima sun lashe kyautar gwarzayen shekara a gasar AMMA.

Jaruma Halima Atete ta samu kyautar gwarzuwar shekara yayin da shi sarakin kannywood, Ali Nuhu ya amshi kyuatar gwarzon mai bada umarni bisa rawar da ya taka a fim din “Mansoor”.

 

Shima Umar M.Sheriff ya samu kyautar matashin jarumi mai tashe a gasar bana bisa nuna basira da yayi a cikin shirin Mansoor.

 

Arewa Music and movies award gasa ce wacce take karrama fitattun yan wasan fim da masu harkar fim tare da mawaka da suka yi fice a ko wani shekara.

An fara gasar ne a cikin shekarar 2014 kuma kamfanin CEMS take daukar nauyin shirya ta.

Taron gasar na bana wanda shine karo na biyar na gasar, ya gudana ne a dakin taro dake nan Soli Center a garin Katsina.

Taron ya samu halarcin dinbim jarumai da mawaka da masu ruwa da tsaki a masana'antar fina-finai. Jarumai da dama sun samu kyaututuka bisa rawar da suka taka a masana'antar nishadantarwa ta arewa.

Ku kasance tare da mu domi samun karin bayanio game da yadda gasar ta kaya tare da jarumai da suka samu mafi yawancin kyauta.