Fashi da makamin garin Offa: Yan sanda na neman tada keyar bayan shugaban majalisar dattawa

0
102

Nigeria's Senate President Bukola Saraki has been summoned for questioning by police

Kamar yadda ya sanar, barayin su biyar daga cikin tawagar da suka kai hari garin Offa sun shaida cewa jagororin ke mara masu baya kan aika-aikan da suke yi.

Rundunar yan sandan Nijeriya na neman shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kan yazo ya wanke kan kan zargin goyon bayan ta'adancin yan fashi da makami da suka far ma bankunan garin Offa na jihar Kwara.

A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Moshood Jimoh ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa yan fashin sun shaida cewa Saraki da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ke mara masu baya wajen aika-aikan da suke yi.

Kamar yadda ya sanar, barayin su biyar daga cikin tawagar da suka kai hari garin Offa sun shaida cewa jagororin ke mara masu baya kan aika-aikan da suke yi.

Bisa ga wannan zargin hukumar take neman sa da ya garzaya ofishin ta dake nan Abuja.

Sakamakon fashi da makami da yan ta'adar suka yi garin Offal, mutane talatin da uku suka rasu ciki har da jami'an yan sanda su tara.

Sai dai Shugabana majalisar dattawa ya mayar da martani bisa wannan gayyatar da zargin da ake masa.

A wata takardar sanarwa da hadimin ya sa hannu, Saraki yayi ikirari cewa wannan mataki ne daga hukumar tsaro na bata sunan shi.

Shi ma a nashi martanin, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya ce zargin da ‘yan sanda ke yi mishi na hannu a daukar nauyin barayi ba shi da tushe balle makama.

NO COMMENTS