A jihar Kano: Gwamna Ganduje ya baiwa masu 'shayi' tallafin N208M

0
172

Gwaman jihar Kano a teburin mai shayi yayin da yake kaddamar da shirin tallafi ga masu sana'ar

Gwamnan ya fadi haka ranar asabar yayin kaddamar da kayan shayi ga matasa a garin Kano.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yace Gwamnatin sa ta tallafawa masu sana'ar shayi 5,200 da naira miliyan 208.

Gwamnan ya fadi haka ranar asabar yayin kaddamar da kayan shayi ga matasa a garin Kano.

Ganduje yace an zabi matasan daga gundumomi 484 daga kananan hukumomi 44 dake jihar.

Ko wanne daga cikin su ya samu kyutar kayayyaki da ya kai kimanin naira dubu arba'in (N40,000).

Gwamnan yace an kaddamar da shirin domin karfafawa matasa tare da taimakawa wajen inganga rayuwar su.

Ko wannen su ya samu kayan abinci da suka hada da kwai, Bournvita, milo madara, taliya, shayi da man geda na kayan tallafi daga gwamnatin jihar.

Daga karshe gwamna ya shawarci su da su kasance suna tsabtace wuraren sana'ar su domin tabbatar da tsabtatacciyar rayuwa kuma su kawarci miyagun kwayoyin da makamancin su.